27 Agusta 2020 - 13:39
Faransa: Dole Ne Gwamnatin Rikon Kwarya A Mali Ta Gaggauta Mika Mulki Ga Farar Hula

Ministan harkokin wajen kasar faransa ya bayyana cewa dole ne gwamnatin rikon kwarya wacce sojoji masu juyin mulki zasu kafa ta gaggauta mayar da gwamnatin ga fararen hula.

ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran reuters ya nakalto Jean-Yves Le Drian yana fadar haka a safiyar yau a ma’aikatar tsaron kasar da ke birnin Prais.Jean-Yves Le Drian ya kara da cewa juyin mulkin ba zai hana sojojin kasar Faransa ci gaba da ayyukansu na yaki da ‘yan ta’adda a kasar ba.Sai dai a tattaunawa tsakanin tawagar kungiyar raya tattalin arzikin kasashen Afirka ECOWAS a ranar 18 ga watan Augustan da muke ciki, sojojin sun ce gwamnatin rikon kwarya a kasar zata dauki shekaru 3 cur kafin su mika mulki ga fararen hula.Kasar Faransa dai tana da sojoji 5100 a yankin Sahel mafi yawansu suna kasar Mali ne.

342/